Tuesday, 15 August 2017

MAGANIN ZAZZABIN TYPHOID ( SANGA-SANGA/RAI-DORI)

GANYEN SANGA-SANGA/RAI-DORI

Assalamu Alaikum
Yau zamu yi magana ne dangane da abinda ya shafi zazzabin Typhoid, yanda ake kamuwa da shi, da yanda za a magance sa.

Zazzabin Typhoid wani ciwon ne mai wuyar sha'ani, da ake daukar sa ta kwayoyin Bacteria mai suna Salmonella typhi. Anfi samun wannan ciwon akasashen masu tasowa. Kungiyar Lafiya ta duniya ta kiyasta cewa mutune miliyan 22 ne a duniya ke fama da wannan zazzabin na Typhoid, haka kuma mutun 200,000 sukan rasa rayukan su akowace shekara. 

ME KE KAWO ZAZZABIN TYPHOID?

Bincike ya nuna ana kamuwa da wannan cutar ta hanyar wasu kwayoyin halitta da ake kira salmonella typhi wayanda ake samun su ta hanyar gurbataccen ruwa, ko abinci marar tsabtaa. Ayayin da mutum yaci wani abinci ko wani abin sha mai dauke da wannan kwayoyin cuta to sukan tafiya zuwa yan hanjin mutum daga nan kuma sai su watsu zuwa cikin jinin mutum inda zasu sami damar yaduwa zuwa hantar mutum da kuma wasu sassa na jikin dan adam daga nan kuma sai su cigaba da hayayyafa.

Bincike ya nuna cewa ba daga shigar kwayoyin cutar suke haddasa ciwo ba, sukan dauki sati daya zuwa biyu kafin mutum ya fara ganin alamomin ciwon su bayyana a gareshi.

ALAMOMIN ZAZZABIN TYPHOID


CIWON KAI: Mutun zai rika fama da ciwon kai akoyaushe, wani ko ya sha magani baya sauka, wani yakan sauka na dan lokaci, kafin ya dawo.


CIWON CIKI: Yawan ciwon ciki alama ce da ke nuna mutun ya kamu da zazzabin typoid, zaka samu kanka da murdawar ciki, wani lokaci har da ciwon mara, zaka ji hanjin ka na kuka wani lokaci har sai mutun ya ziyarci bayi da sauran su.

RASHIN KUZARI: Mutun zai kasance akoyaushe ba shi da wani kuzari, aiki kadan zai yi sai gajiya.

Rashin jin dadin abinci yana daya daga alamomin kamuwar cutar typhoid

YANDA SANGA-SANGA KE MAGANCE ZAZZABIN TYPHOID

Masana maganin gargajiya sunyi gwaji akan yanda ganyen sanga sanga ke maganin zazzabin typooid. 

Za asamu ganyen sanga sanga a wanke sa da ruwa masu tsabta, atafasa sa. Bayan an tafasa za a sauke a tace ganyen in ya huce a maida su ruwan sha.

Akan daka ganyen sa a tace ruwan ba tare da an tafasa ba.

Akan yi kunu da shi ana sha, ana kuma iya dafawa arika suraci da wanka da shi. 

Bayan  maganin ciwon typhoid da sanga sanga ke yi, bincike ya nuna cewa sanga sanga yana kashe kwayoyin plsmodium musamman falcifarum dake kawo zazzabin malaria na cizon sauro wato dai baya ga kasancewa sanga sanga na maganin typhoid to kuma yana maganin malaria.

RIKAKAFE


Mu kula da tsabtace muhallin mu, musanman ruwan shan mu, da kuma abincin mu. Mukan iya tafasa ruwan mu na sha kafin muyi amfani da su, wannan hanya ce sosai da za ta taimaka wurin rage yaduwar wannan ciwo. haka kuma rage cin abincin sayarwa Wanda ba a tabbatar da tsabtar sa ba.
Allah ya bamu lafiya yasa mu dace.

Friday, 28 July 2017

LABARIN SOYAYYAR LAILA DA MAJNUN


Waye Majjnun Lailah?



Wani mutum ne da aka yi a daular Banu Umaiyya abisa zance mafi inganci. Sunansa shine Qais Ibn Mulawwah daga kabilar Banu Amir, Qais balaraben kauye ne, ya taso tare da ‘yar gidan kawunsa mai suna LAILA BNT MAHDI IBN SA’D Amfi sanin Laila da sunan Laila Aamiriya, tare suka taso tun suna yara suna kiwon dabbobi har suka girma, suka fita daga sahun yara suka kai munzalin balagha.

A Yayin da alamun nuna balaga da cikar budurci suka gama bayyana ajikin Laila sai Qais ya rude soyayyarsa gare ta, hankalinsa ya dugunzuma ya tashi. Domin a wannan lokacin ne Qais ya Llura da irin kyawun dirin da Allah ya yiwa abokiyarsa Laila, a kullum soyayyar Laila sai kara tashin gwauron zabi take yi a cikin zuciyar Qais, a cikin wannan yanayi ne Qais ya shiga rera mata waqoqin soyayya kala-kala babu dare babu rana hakance tasa Mahdi mahaifin Laila ya nemi da Qais ya fito dan maganar aure, saboda nuna soyayya da kauna said a Qais ya bayar da raquma hamsin gidansu Laila a matsayin kudin Aure.

Ana haka sai ga wani mutum da ake kira WIRD BN MUHAMMAD wani dan hamshaqin attajiri ne daga cikin masarautar Banu Umaiyya, katsahan yayi ido hudu da Laila a wata rana a cikin wani Lambu tana kiwon dabbobinta. Daga wannan ranar Soyayyar Laila ta hana Wird ya yi bacci a wannan dare! Cikin yan kwanaki kadan Iyayenm Wird suka sauka a gidan su Laila dan neman aurenta ga dansu Wird. A wannan rana da Iyayan Wird suka je ga mahaifin Laila saida suka ajiye masa Manyan Raquma guda dari (100) a matsayin kudin aure, wato ribi biyu akan abinda Qais ya bayar!

Daga nan lissafi ya kwacewa mahaifin Laila, domin kuwa yayi irin mugun abin kunyar nan na nuna kwadayi da son abin duniya. Bayan haka ne Mahaifin Laila ya kira ‘yarsa Laila cikin daki yanai mata hudubar cewar ga mai kudi dan masu mulki shi zai aurawa ita! Babbar Magana! Laila taki amincewa da maganar mahaifinta a karon farko, amma sai ya yi mata barazanar cewar zai yanka ta idan har bata amince da auren Wird ba. katsam sai aka wayi gari Qais ya ji gari ya dauka da kace nace din anyiwa masoyiyarsa Laila aure da Wird. Wane irin hali Qais zai kasance a wannan ranar? Tun daga wannan lokacin bacci yayi hijira daga idonsa, farin ciki ya gagari zuciyarsa, damuwa bakin ciki gami da bacin Rai da takaici, zubar da hawaye babu dare babu rana, suka kasance tare da Qais a matsayin abokai na din-din-din!

Wake waken soyayya sune zancensa, bashi da abokin hira sai wakar da yake yiwa laila ga kadan daga irin abinda yake cewa: zuwa ga Allah nake kai kukan son laila kamar yadda maraya yake kai kukan maraicinsa zuwa a Allah. Marayanda da kafarsa ta karye gashi kuma dangi sun gujeshe, Lallai rasa iyaye abune mai girman gaske. Haka Qais da aka yiwa lakabi da “Majnunu lailah” yake bin kwararo kwararo da saman manyan duwatsu da bakin ruwa da cikin furanni yana rerawa Laila wadannan baituka masu motsa zuciya bai gushe ba harse da akayi masa lakabi da “majnunu laila”....!

Duk da cewa itama Laila tana matukar son Qais(majnun) amma kuma hakan baya hanata ta wahalar dashi, a wasu lokutan ma harda yi masa wulaqanci, baya ga yin amfani da mallakeshi da tayi wajen azabtar dashi, dama haka sha’anin mata yake shi yasa majnun awani baiti yace:

“Nace da wani babban malami da na gamu dashi a makka, dan Allah ka bani labarin wacce take cutar dani, azamanin da take jiji da kai (saboda ina sonta) shin hakan da take ba laifi bane?” Sai Malamin ya fadawa Qais cewa: “Wallahi da sannu azaba zata shafe ta kuma a duniya ma saita hadu da bala’I”. Daganan Qais yace, sai na kasa mallakar idona sai da hawaye ya zubo cikin sauri ya jiqa min aljihun rigata, sai nace, Allah ya yafe mata laifinta duk da yake a duniya dan kadanne samunta.

Qais ko Laila Majnun Bai gusheba a cikin wannan hali har sai da ya samu tabin hankali. Domin ya kasance idan yaga yara suna wasan kasa yakan zauna tare dasu ya taro kasa ya rinqa gina gida irin wanda yara suke yi da kasa yana cewa cikin waqa: “abokaina kuzo kuga gidana nida laila”....!

A yayinda al-amari ya tsananta sai mutane suka baiwa mahaifin Majnun wato Qais shawara da ya daukeshi ya kaishi ka’aba (dakin Allah) ya umarce shi da ya roqi Allah ya cire masa son Laila! Amma saboda tsananin soyayya a yayin da suka je dakin ka’aba sai mahaifinsa yace masa: kama tufafin ka’aba ka roki Allah ya cire maka son Laila sai Majnun ya kama yace: “Allah na tuba gareka daga dukkan laifi, amma bazan tuba daga son da nake yiwa Laila ba . . . ataqaice haka majnun ya rayu cikin wannan yanayi na abin tausayi!

Ita kuwa Laila tuni wanda ya aureta ya dauke daga kasar Saudiyya gabaki daya zuwa kasar Iraqi. Haka itama ta rayu cikin wannan mummunan yanayi abinka da ‘ya mace mai rauni saida rashin ganin Qais ya haddasa mata ciwon zuciya .......! Daga nan ita ma ta kamu da ciwon zuciya saboda tsananin soyayyar Qais Majnun! Tana cikin wannan hali ne na rashin ganin masoyinta Allah ya karbi rayuwarta! A lokacin da Majnun yaji labarin rasuwarta sai da yaje har kasar Iraqi ya nemi inda take, da inda aka binne ta, a makabartar da aka binne laila a daidai gindin kabarinta ya tare.....! Bashi da aiki sai kuka da wakokin soyayya a gareta. Wata rana da safe sai masu wucewa suka hangoshi (Qais-Majnun) ya kifa cikinsa akan qabarinta, ko da aka zo aka duba sai aka tarar Allah ya yi masa cikawa!.


Haka Allah yake jarabtar wasu da soyayya, wasu ajarab ce su da sauki wasu kuma akasin haka. Ya Allah muna rokon ka kada ka jarabce mu da abinda zukatan mu basa iya dauka, ya kuma kare mu da kwadayi da son abin duniya.

MUNA MARABA DA COMMENTS DINKU


  


  ALAMOMI 16 DA ZA SU TABBATARWA NAMIJI MACE TANA MATUKAR SONSA


1. KALLO:  Mata suna aika sakonni da yawa ta hanyar kallo, kamar So, raini, tsoro, ba ruwana dakai da sauransu, kuma kowane ba sai an fassarawa mutum ba da ya gani yasan me ake nufi

2. KULAWA: Wannan na nufin ta nuna ta damu dashi a kowanne lokaci, ta hanyar kokarin jin halin da yake, lafiyarsa da kuma al'amuransa. Ko yana kusa da ita ko kuma nesa da ita. Idan abun murna ya sameshi ta tayashi idan na jaje ya sameshi ta jajanta masa. Ba shakka wannan yana nuna soyayya.

3. BIYAYYA: Mace ta rinka girmama namiji, abokansa da 'yan'uwansa a duk lokacin da zata mu'amalance shi ko su, a gaisuwa ne, a magana ce, a rubutaccen sako ne duk wadannan yana bukatar yaga ladabi acikinsu kada ta rinka yi masa tsiwa da rashin kunya da sauran dabi'u da zasu nunawa mutum ba a dauke shi abakin komai ba.

4. HAKURI: Babban abinda yafi bada wahala  a mu'amala kuma a kafi jarraba mutum akai shine hakuri, ya zamanto namiji ya gamsu da hakurin mace ta kowace hanya kar ta rinka yi masa koke-koke, ko ta zama mai rainuwa, duk abinda ya bata tayi hakuri dashi kar tace bai kai kaza ba ko kuma bai kai na wance ba, idan sabani ya shiga kada tayi jayayya dashi idan kuma taga yayi fushi ta rarrasheshi tace yayi hakuri.

5. UZURI: Anan ana nufin mace ta zama mai karbar hanzarinsa duk lokacin da wani abu ya faru, misali, ta buga masa waya bai dauka ba ko ta tura masa sako bai bata amsa ba, kada tayi fushi tace shikenan tunda abin wulakancine bazan sake kira ba, ta daure ta cigaba da neman jin me yake faruwa kafin ta yanke hukunci, domin akwai dalilai da yawa dake iya sa hakan ta kasance kamar rashin lafiya, faduwar wayar da sauransu. Idan kuma ya kirata daga baya shima ta dauka cikin farin ciki ba da fushi ba, har taji dalilinsa, kuma koda ya kawo mata hujja ta karya kuma ta gane to tayi dariya acikin ranta kawai kada ta nuna masa ta harbo jirginsa.

6. TAUSAYI: Mace ta zama mai tausayawa namiji don shi namiji har kirari ake masa da cewa "Zakara mai neman suna, bada kwaya kaci tsakuwa" saboda haka ta kalli wane shi da idan basira kamin ta koro masa wasu bukatun, kada tasa ya rinka jin tsoron zuwa gurinta, ko kuma da yaga kiranta gabansa ya fadi don yasan matsala za'a karanta masa. Wani kuma ba dora masa bukatar za a yi ba a'a, shi zai dorawa kansa amma zai kokarin yin abinda yafi karfinsa don kar ace ya gaza ko kuma ace kai wane BA dama! Da sauran dalilai, to shi wannan birki za tai ta taka masa.

7. TATTALI: Duk abinda namiji ya yiwa mace tayi kokarin tattala wannan abun, kada ta zama mai barna ko almubazziranci don gadarar ko yanzu nace ya sake yimin zaiyi.

8. SHAWARA: Idan namiji yaga a mafi yawancin lokaci mace takan shawarceshi acikin wasu lamuranta na rayuwa wanda shi yasan ba lallai bane ta sanar dashi kuma yasan ba wani abinsa take jira ko sa rai ba kuma bashi kadai ya iya bada shawaraba, to wannan yana bashi sakon cewa ana tare dashi.

9. ALFAHARI: Wato mace ta nunawa namiji shi wani ne a gurinta, a gaban kowa, ko an tambayeta ko ba a tambayeta ba, ba idan anji tana waya dashi a tambayeta wane tace 'wani ne yake ta damuna nace ya daina kirana amma yaki' ko kuma tace 'saurayin kawatane' muke gaisawa. A'a tace ni da (Baraune) ta fadi sunansa.

10. KYAUTATA ZATO: Mace ta yiwa namiji zato na alkhairi kada ta munana masa zato ko tai ta kokarin gano wadansu kura-kurensa koda kuwa yanayi, matukar ya sirrintasu har sai idan yaqini ya zo mata.

11. YAFIYA: Babu yadda za'ayi a gina mu'amalar da sabani bazai shigo ba, don haka mace ta zama me afuwa ga namiji a duk lokacin da sabani ya yazo, kada ta dage akan lallai ita tana da hakki, koda tana dashi din ta yafe wannan zai kara mata daraja ko ba a sannan ba ko zuwa gabane, kuma kada a yafe a baki amma a zuciya.... Ko kuma ranar da wani sabanin yazo ace dama rannan ma ... Kada tayi haka.

12. KYAUTATAWA: Ya zamana duk lokacin da zaije wajenta to ta kyautata masa kada yaji cewa bata mutuntashi ba.

13. KARIYA: Shine mace ta zama me kare namiji daga dukkanin abinda zai cutar dashi ko kuma mutuncinsa, ya zamana wani ko wata bazai ci zarafinsa ba matukar tana wurin koda kuwa danuwantane.

14. TSAFTA: Ya zamana duk lokacin da namiji zai hadu da mace to ya ganta kamar sannan za'a kaita gidan miji .......

15. NUTSUWA: Mace ta zama mai sa namiji farin ciki a koda yaushe, har ya zamto koda an bata masa rai a wani gurin ko kuma wasu alamuran sun sha masa kai zai iya zuwa gurinta ko kuma kiranta suyi maganar don yasan zata rarrasheshi har ya sami nutsuwa da kwanciyar hankali.

16. GASKIYA: mace ta kasance mai  bayyanar da gaskiyarta ga namiji a duk abinda za suyi, kada karya, cutarwa, rashin gaskiya ya fito a gurinta komai kankantarsa

Muna maraba da omments din ku,  na wasu daga alamomin da ba mu fada ba. Ku biyo mu a post din mu da ke nan tafe. 

Thursday, 27 July 2017

 KO ME YASA MATA KE NEMAN YAN UWAN SU MATA?



Madigo wata hanya ce da Mace zata biya bukatar ta ga yar uwarta Mace, ta hanyar sunbatar juna, shafe-shafe, rungume-rungume, da duk wani abun da zai  kwantar masu da sha’awar su ko kuma ya gamsar da su. Mafi yawan Matan da ke wannan sana’ar suna afkawa wannan ibtila’in ne a sanadiyar kawance da masu irin wannan dabi’on, wasun su kan fada ne a sanadiyar kwadayin abin duniya, wasu rashin yin Aure da sauran su.

Wata yar Madigo da nayi hira da ita, ta shaida min dalilin tana afkawa wannan harkan. Ta ce “Maigidana ya kasance mutun ne mai son kai, ba ya  damu da biyan bukata taba, daya samu biyan tasa bukatar”. Ta ci gaba da cewa “Mu na zaune ahakan har zuwa lokacin da na nemi ya sake ni. Bayan mun rabo na hadu da wata da muka kulla kawance, har ta kai ta tare a gidana, daga nan muka fara biyawa junan mu bukata. Da na tambaye ta ko zata koma wa uban yayanta? Sai tace “Hmmmm! Ba  zaki gane ba, wallahi san yanzu bana sha’awar Namiji”.

ALAMOMIN MASU MADIGO


1. Zaki ga mafi yawan masu wannan dabi’ar suna saka sarka a kafar su. Ba lallai bane duk wanda ya sa sarka a kafa ya kasance dan madigo, wasu kan sa ne saboda suna da ra’ayin hakan


2. Mace ta yawaita yabon kyawon fuskar ki da na diran jikin ki. Yar uwa ki kiyaye duk macen da takan yawaita yabon dirar jikin ki ko kyan fuskar ki, to akwai ayar tambaya gane da ita

3. Sanya zobe a yatsun kafa tabi’a ceta masu yin madigo, ta hanyar wannan alama ce za su gane junan su. Akan samu wasu matan da ke da ra’ayin sanya zoben ba tare da sanin aibin sanyawar ba.

4. Za kiga mace tana da kawaye mata da suke yawan  ziyarta ta ko kuma ita tana yawan zuwa wurin su, ana shegewa dakin ana shewa da tabe-tabe. Yar uwa ki guje shiga cikin irin wayan nan kawayen.

5. Yar uwa ki guje kawar da bata jin kunyar sakin al’aurarta a gabanki, ko kuma mai yawan kalle-kalle fina-fina na batsa ko kuma na yan madigo.

6. Ki guje kawar da take yawan kai maki runguma, ko ta rika kallun kirjin ki a lokacin da kika yi kuskuren sakin wani sashe na tsiraicin ki.

ILLOLIN YIN MADIGO

Madigo yana daya daga cikin manyan laifukan da Ubangiji ya kyamata, sai dai shari’ah bata bada ainihin wani hukuncin da za’ayi wa masu madigo. Sai dai mafi yawan malamai suna ganin za’ayi masu hukunci dai-dai da na yan luwadi.


1. Akan iya daukar cutukan zamani ta hanyar madigo.

2. Yin madigo yana raunana imanin mutum

3. Yana gusar da kunya gaba daya

4. Fushin Allah ga masu wannan aikin

5. Gushewar mutunci a idon mutanen kirki

6. Masu yin wannan aiki sukan samu kansu a cikin kuncin rayuwa

7. Rashin yin kyakkyawan karshe ga masu aikata madigomadigo

8. Rashin sha’awar Aure

9. Za a kai lokacin da mace bata sha’awar namiji gaba daya


HANYOYIN BARIN MADIGO

Wajabi ne ga duk masu irin wannan dabiar ta madigo da suji tsoron Allah su nisantar da kan su ga barin yinsa. Su tuna ko wane lokaci za su iya riskar mahaliccin su bayan suna aika wannan mummunar aikin. Yar uwa ga kadan daga cikin hanyar da zaki bi ki nisanci kanki da wannan dabi’on.

1.  Ki tuba da niyar ba zaki sake aikata wannan aikin ba

2.  Ki nisantar da kanki ga duk wata kawa da kuke wannan harkan

3.  ki yaawaita istigifari

4. A duk lokacin da sha’awar yin hakan ya taso maki, ki yi alwala ki karanta daga abinda ya  sauwaka na daga Qur’ani.

5. Nisanta kan ki ga kallun fina-finan  da hoto nan batsa

6. ki rika sawa ranki azabar da ke cikin yin maddigo, a duk lokacin da sha’awar yin hakan ya   ta so maki

7. ki yawaita yin azumin Litinin da Alhamis

8. ki tuna kusancin Ajalinki, kwanciyar kabari, hisabi da kuma makomar masu irin laifin ki.

Ya Allah muna tawassali da sunayen ka kyawawa da ka kiyaye mu da fadawa cikin wannan halin, ka shiryar da masu yi, ka gafarta mana ka kuma anshi tuban mu.

Ina mai farin cikin samun comment dinku game da shawarwari, illoli, da alamun da za agane masu wannan harkan wanda ban kawo ba.

Wednesday, 26 July 2017

     ALAMOMI 10 DA ZAKI GANE IN NAMIJI NA SONKI

So da yawa mukan kasa fahimtar ko namiji ya na son mu, ko kuma shakuwa ce da abotaka tsakanin mu da su.Ga kadan daga cikin wadan su alamomin da za su tabbatar maki lallai Namiji na son ki, so kuma na gaskiya da soyayya.

1. TAUSAYI
Wani feeling ne da ke ratsa zuciyar duk wani namiji da ya kamu da ciwon son mace. Tausayi yana daya daga matakan farko da ke tabbatar wa mace lallai namiji yana gab da, ko kuma ya kamu da sonki. Zaki ga abu kadan  wanda bai taka kara ya karya ba, namiji yana tausayawa mace, ciwo kadan zaki ga yana nuna matukar kulawar sa da tausayin sa gare ki. Yar uwa ki kula duk namijin dayaya jin tausayin ki, toh da wuya yana maki son gaskiya. 
 
2. SADARWA
Idan namiji yana matukar sonki, za ki rika samun kiran wayar sa akoda yaushe, baya iya zama na tsawon lokaci ba tare da ya kira yaji lafiyar ki ba. YakanYakan
 so ki zama farkon wacce zai yi Magana da ita bayan tashin sa daga bacci, haka kuma ta karshe da zai yi sallama da ita kafin ya kwanta. Zaki rika samun sakon sa na wayar sadarwa(SMS). Haka kuma idan kika masa flashing duk abinda yake yi zai ajiye sa, ya kira wayar ki, ko ya dawo maki da  sakon da kika tura masa. Yar uwata ki kula namijin da baya damu da ya kira ki ba, sai in ke kin gaji dan kanki kin kira sa, ko kin tura masa sako, toh baki cancanci bata lokacin ki garesa ba.

3. KASANCEWA DA KE
Namiji kan so kasancewa tare da wacce yake so akoda yaushe, baya gajiya da ganinta, duk yanda ba yada lokaci zai saman maku lokaci don kasancewa tare da ita. Duk namijin da baya kiran ki, sai dai ke dan kanki ki nemi ko hado, toh shima yar uwa ina maki tsoron in wannan namijin da gaske yana sonki. Saboda wanda ke sonki na gaskiya, yana son kasancewa da ke

4. SATAR KALLUN KI
Namijn da ya kamu da sonki, baya gajiya da kallun ki. Idan kuna tare ki kula, abu kadan zaki yi, zai tsora maki ido, wani lokaci ma zaki kama sa yana satar kallun ki. Haka kuma zai rika kokari ya tausasa idon sa wurin Magana da ke, in kika kula zaki iya hango tausayi da soyayya a idon sa. 

5. GABATAR DA KE GA FAMILY SA
Duk Namijin da ke kaunar ki saboda Allah, zaiyi kokarin gabatar da ke ga yan uwansa da abokanin sa. Baya jin kunya ko wani haufin nuna ki a matsayin wacce yake so, yake kuma fatan zama uwar 'yayan sa. Yar uwata ki kula, duk namijin da kike zaune da shi, yana maki boyon kisan asalin sa, ko iyayen sa, da abokanin sa, toh wannan namiji yana da wata manufa daban gareki, yar uwa kiyi hakuri ki kama gaban ki, ina shaida maki zai bata maki lokaci ne ga banza. 

6. YARDA DA AMINCI
Namiji na yarda da amincewa ga macen da yake so. Zai rika gaya maki sirin sa, musamman dangane ga abinda ya shafi aikin sa. Zai gaya maki sirri kansa da yake tsoron gayawa abokanin sa, saboda ya yarda da ke, baya taba tunanin zaki tuni asirin sa. Idan namiji na maki boye boyen sirrukan sa, toh ki bincike son da yaje maki.

7. KYAUTA
Kyauta na daya daga cikin alamomin da za su tabbatar maki cewa Namiji na sonki, so na gaskiya. Wanda ke sonka baya jin kiwar ma kyauta, ko da ko mutunen nan talaka ne, akoyaushe fatan sa yayi abinda zai faranta maki rai, ta hanyar saya maki wani abu ko mai kankantar sa, muddin yasan zai sayya ki farin ciki. Sai dai ba lallai bane asamu ko wane namijin a hakan, saboda shish alkhairi daga jini ne, wani duk son da yake maki, sai ki same sa marowaci, baya iya wa ko kansa alkhairi balla ya yi maki. Yar uwa sai ki kula in dai kin samu wasu daga cikin alamomin da a ka kawo, amma kuma kin same sa da halin rashin maki kyauta, sai kiyi hakuri, rowar ajinin sa take.

8. ABOKANI
Abokani suna daga cikin alamomin da zaki fahimce cewa namiji yana kaunar ki. Ki kula in abokanin sa na gayama ki cewa baya da aiki sai masu hirar ki, abo kadan zai ce "wance kaza" toh wannan mutum yana sonki.

9. TSARA RAYUWAR SA DA KE
Yar uwa ki lura, a duk lokacin da kuna tare da shi, yana kawo zancen auren ku, kamar ya ce maki; lokacin auren mu za ayi kaza, ko kuma yayan mu kaza, ya na dai kokari tsara rayuwar sa tare da ke. Toh wannan mutunen yana maki so na gaskiya, so kuma na Aure.

10.  SHAN MINTI
A duk lokacin da Namiji yake nuna zalamar sa gareki, kamar son yayi maki kiss, ko ya rungume ki, toh wannan ba saurayin kwarai ba ne. Duk namijin da ke sonka sabida Allah, yake kuma muradin ki zama uwar 'yayan sa, ba zai fito maki da kwadayin sa a fili ba, har yana kokarin ya sa ki sabawa ubangijin ki. Yar uwa ki kula da irin dangin wayan nan samarin na zamani, saboda su suka yi yawa awannan lokacin. Kina kuskuren da kika bari ya fara taba ki da sunan wai ya nuna maki yanda yake jinki a ransa, ta hanyar rungumar ki, ko yi maki kiss, toh tabbas shaidan zai shiga, har ya kai ku da ku afkawa juna, daga nan duk son da yake maki zai guje ki, muddin ya samu abinda ya ke so. In kuma ma Allah ya kaddari ku kayi auren ba wani mutuncin ki zai gani ba, zai kuma rika zargin ki. Yana tunanin bada shi kadai kika saba ba. Yar uwa ki kula, in wannan bai taba farowa da ke ba, na tabbatar da ya faro da kawar ki ko yar uwar ki.

Daga karshe duk wanda ke da wasu alamu da za su tabbatar mana cewa Namiji yana son mu, sai ya danna akwati mai dauke da 'leave reply'. Ina maku fatan alkhairi da samu abokanin rayuwa na kirki wanda za su so ki, so na gaskiya.

Ku saurare rubutuna akan yanda zaki mallaki zuciyar saurayin da kike so, ba tare da kin gaya masa ba.