ALAMOMI 10 DA ZAKI GANE IN NAMIJI NA SONKI
So da yawa mukan kasa fahimtar ko namiji ya na son mu, ko kuma shakuwa ce da abotaka tsakanin mu da su.Ga kadan daga cikin wadan su alamomin da za su tabbatar maki lallai Namiji na son ki, so kuma na gaskiya da soyayya.
1. TAUSAYI
Wani feeling ne da ke ratsa zuciyar duk wani namiji da ya kamu da ciwon son mace. Tausayi yana daya daga matakan farko da ke tabbatar wa mace lallai namiji yana gab da, ko kuma ya kamu da sonki. Zaki ga abu kadan wanda bai taka kara ya karya ba, namiji yana tausayawa mace, ciwo kadan zaki ga yana nuna matukar kulawar sa da tausayin sa gare ki. Yar uwa ki kula duk namijin dayaya jin tausayin ki, toh da wuya yana maki son gaskiya.
2. SADARWA
Idan namiji yana matukar sonki, za ki rika samun kiran wayar sa akoda yaushe, baya iya zama na tsawon lokaci ba tare da ya kira yaji lafiyar ki ba. YakanYakan
so ki zama farkon wacce zai yi Magana da ita bayan tashin sa daga bacci, haka kuma ta karshe da zai yi sallama da ita kafin ya kwanta. Zaki rika samun sakon sa na wayar sadarwa(SMS). Haka kuma idan kika masa flashing duk abinda yake yi zai ajiye sa, ya kira wayar ki, ko ya dawo maki da sakon da kika tura masa. Yar uwata ki kula namijin da baya damu da ya kira ki ba, sai in ke kin gaji dan kanki kin kira sa, ko kin tura masa sako, toh baki cancanci bata lokacin ki garesa ba.
3. KASANCEWA DA KE
Namiji kan so kasancewa tare da wacce yake so akoda yaushe, baya gajiya da ganinta, duk yanda ba yada lokaci zai saman maku lokaci don kasancewa tare da ita. Duk namijin da baya kiran ki, sai dai ke dan kanki ki nemi ko hado, toh shima yar uwa ina maki tsoron in wannan namijin da gaske yana sonki. Saboda wanda ke sonki na gaskiya, yana son kasancewa da ke
4. SATAR KALLUN KI
Namijn da ya kamu da sonki, baya gajiya da kallun ki. Idan kuna tare ki kula, abu kadan zaki yi, zai tsora maki ido, wani lokaci ma zaki kama sa yana satar kallun ki. Haka kuma zai rika kokari ya tausasa idon sa wurin Magana da ke, in kika kula zaki iya hango tausayi da soyayya a idon sa.
5. GABATAR DA KE GA FAMILY SA
Duk Namijin da ke kaunar ki saboda Allah, zaiyi kokarin gabatar da ke ga yan uwansa da abokanin sa. Baya jin kunya ko wani haufin nuna ki a matsayin wacce yake so, yake kuma fatan zama uwar 'yayan sa. Yar uwata ki kula, duk namijin da kike zaune da shi, yana maki boyon kisan asalin sa, ko iyayen sa, da abokanin sa, toh wannan namiji yana da wata manufa daban gareki, yar uwa kiyi hakuri ki kama gaban ki, ina shaida maki zai bata maki lokaci ne ga banza.
6. YARDA DA AMINCI
Namiji na yarda da amincewa ga macen da yake so. Zai rika gaya maki sirin sa, musamman dangane ga abinda ya shafi aikin sa. Zai gaya maki sirri kansa da yake tsoron gayawa abokanin sa, saboda ya yarda da ke, baya taba tunanin zaki tuni asirin sa. Idan namiji na maki boye boyen sirrukan sa, toh ki bincike son da yaje maki.
7. KYAUTA
Kyauta na daya daga cikin alamomin da za su tabbatar maki cewa Namiji na sonki, so na gaskiya. Wanda ke sonka baya jin kiwar ma kyauta, ko da ko mutunen nan talaka ne, akoyaushe fatan sa yayi abinda zai faranta maki rai, ta hanyar saya maki wani abu ko mai kankantar sa, muddin yasan zai sayya ki farin ciki. Sai dai ba lallai bane asamu ko wane namijin a hakan, saboda shish alkhairi daga jini ne, wani duk son da yake maki, sai ki same sa marowaci, baya iya wa ko kansa alkhairi balla ya yi maki. Yar uwa sai ki kula in dai kin samu wasu daga cikin alamomin da a ka kawo, amma kuma kin same sa da halin rashin maki kyauta, sai kiyi hakuri, rowar ajinin sa take.
8. ABOKANI
Abokani suna daga cikin alamomin da zaki fahimce cewa namiji yana kaunar ki. Ki kula in abokanin sa na gayama ki cewa baya da aiki sai masu hirar ki, abo kadan zai ce "wance kaza" toh wannan mutum yana sonki.
9. TSARA RAYUWAR SA DA KE
Yar uwa ki lura, a duk lokacin da kuna tare da shi, yana kawo zancen auren ku, kamar ya ce maki; lokacin auren mu za ayi kaza, ko kuma yayan mu kaza, ya na dai kokari tsara rayuwar sa tare da ke. Toh wannan mutunen yana maki so na gaskiya, so kuma na Aure.
10. SHAN MINTI
A duk lokacin da Namiji yake nuna zalamar sa gareki, kamar son yayi maki kiss, ko ya rungume ki, toh wannan ba saurayin kwarai ba ne. Duk namijin da ke sonka sabida Allah, yake kuma muradin ki zama uwar 'yayan sa, ba zai fito maki da kwadayin sa a fili ba, har yana kokarin ya sa ki sabawa ubangijin ki. Yar uwa ki kula da irin dangin wayan nan samarin na zamani, saboda su suka yi yawa awannan lokacin. Kina kuskuren da kika bari ya fara taba ki da sunan wai ya nuna maki yanda yake jinki a ransa, ta hanyar rungumar ki, ko yi maki kiss, toh tabbas shaidan zai shiga, har ya kai ku da ku afkawa juna, daga nan duk son da yake maki zai guje ki, muddin ya samu abinda ya ke so. In kuma ma Allah ya kaddari ku kayi auren ba wani mutuncin ki zai gani ba, zai kuma rika zargin ki. Yana tunanin bada shi kadai kika saba ba. Yar uwa ki kula, in wannan bai taba farowa da ke ba, na tabbatar da ya faro da kawar ki ko yar uwar ki.
Daga karshe duk wanda ke da wasu alamu da za su tabbatar mana cewa Namiji yana son mu, sai ya danna akwati mai dauke da 'leave reply'. Ina maku fatan alkhairi da samu abokanin rayuwa na kirki wanda za su so ki, so na gaskiya.
Ku saurare rubutuna akan yanda zaki mallaki zuciyar saurayin da kike so, ba tare da kin gaya masa ba.
54 comments:
Allah Ya hadamu da na kirki
Ameen
Allah yabamu
nagari
Gaskiya ansamu matsala sonda yakemun inconclusive ne.
Kanawan dabo 😂😂😂😂
Alla yahadamu dana kwarai
Alla yahadamu dana kwarai
Enter your comment...naji dadin wannan shawarwarin ku nagode.
Allah kahadamu da maxa nagari
Hhhh wato inconclusive bai cikaba kenan ? 😃😃🤣
Mungode sosai
Muna godiay
Gaskiya nima nawa inconclusive ne
ameen zance muma maza Allah ya bamu mata nagari
Allah kahadamu da masu sonmu nagaskiya
Ina so na iya soyayya da ssurayina
Thank you so much
ykk nagode amma inason ki Kara rybutomin wasu daga ciki
Usman
ykk Allah yabamu nagari
Amma banji ansa abu dayaba
Idan ina waya da baby ta tana yawan kashe wayana ta dauki wani wayan amma kuma idan nakirata tana waya bata daukan wayan bayan ta gama baxata kiraba saide nida na damu nakira ya wannan lissafin yake slm
gaskiya bata damu da kaiba Kuma akwai Wanda ta ke so
Ameen
Allahya hadamu da masoyya nnagare
Gasky min gd dasha wararki
Inason wani amma naka sa gaya mai
Toh mungode Allah yasamusamu abinda mukeso
Alhamdulilah
Alhmdllh
Kaiiii wlh gaskiya ne
Alhmdllh
Dama karki fada Mai ki daiyi kokarin yanda Zaki samu phone number en shi kice kina son ki Zama frnds daga Haka kina dai nuns kin damu dashi da kula maybe kafun kice kina son shi , shi zaice Yana zon ki Allah ya taimaka
Thanks
Allah kkaremu Dyan Shan minti, Kai mama xabi ngari, tank u so much sis.
mungode
Amin y hayyu y kayyum
Amin y Allah ka hadamu da abokan xama na gari🤲🙏
Thanks
Pls answers
A bani tshawara Dan Allah
Yaudara yayi yawa gurin yan mata yanzu
Inason saurayi Amma Nandan yadda xangayamaiba Kuma muna ways dashi sosai
Ameen ya Allah
Ameen don son annabi,,,,
Allah ya hadamu da nagari👏
Nima inason wani Amma muna magana dashi ta snap Amma wani time din idan namai mgn baya yawan maido mon reply Wana Irin. Abu xanrinka Yi domin yaji na birgeshi aban shawara
Ni Kuma abokin yayana nakeso wlh sosai Amma narasa yazanyi yagane basai nafada mashi da kaina ba yagano sai yace Yana sona Amma haryanxu ji nake kmr na mutu wlh
Ni inada phone din tsoro nakeji Amma zan iya kiranshi Amma Muna mgn ta chart Muna gaisawa har shawara nake Nema gurinshi Kuma yabani
Kawai kifadaman mashi
Kina sansa
Nima akuai tsohom saurayina murrabu dashi tsawun shekara Amma haryanzu inasomsa meyekamta inyi Kuma bani da ko phone number dinsama
Amen ya allah allah yabarmu damasu sonmunagaskiya
Kinaima kikirashi kice kinkirasa ne kugaisa ga phone number na muyi magana 0707 820 4897 kimin magana pls inkuma ta WhatsApp ne zakiyimin magana ga number danake amfani dashi 07043610988
Kici gaba karki fadamai kijirashi zaifada maki dakansa
Gaskiya karki fadamishi ze iya wulaqantaki
Ni banson Inga macce na son namiji Allah karka jaraceni da hk
Post a Comment