MAGANIN ZAZZABIN TYPHOID ( SANGA-SANGA/RAI-DORI)
![]() |
GANYEN SANGA-SANGA/RAI-DORI |
Assalamu Alaikum
Yau zamu yi magana ne dangane da abinda ya shafi zazzabin Typhoid, yanda ake kamuwa da shi, da yanda za a magance sa.
Zazzabin Typhoid wani ciwon ne mai wuyar sha'ani, da ake daukar sa ta kwayoyin Bacteria mai suna Salmonella typhi. Anfi samun wannan ciwon akasashen masu tasowa. Kungiyar Lafiya ta duniya ta kiyasta cewa mutune miliyan 22 ne a duniya ke fama da wannan zazzabin na Typhoid, haka kuma mutun 200,000 sukan rasa rayukan su akowace shekara.
Bincike ya nuna ana kamuwa da wannan cutar ta hanyar wasu kwayoyin halitta da ake kira salmonella typhi wayanda ake samun su ta hanyar gurbataccen ruwa, ko abinci marar tsabtaa. Ayayin da mutum yaci wani abinci ko wani abin sha mai dauke da wannan kwayoyin cuta to sukan tafiya zuwa yan hanjin mutum daga nan kuma sai su watsu zuwa cikin jinin mutum inda zasu sami damar yaduwa zuwa hantar mutum da kuma wasu sassa na jikin dan adam daga nan kuma sai su cigaba da hayayyafa.
Bincike ya nuna cewa ba daga shigar kwayoyin cutar suke haddasa ciwo ba, sukan dauki sati daya zuwa biyu kafin mutum ya fara ganin alamomin ciwon su bayyana a gareshi.
ALAMOMIN ZAZZABIN TYPHOID
CIWON KAI: Mutun zai rika fama da ciwon kai akoyaushe, wani ko ya sha magani baya sauka, wani yakan sauka na dan lokaci, kafin ya dawo.
CIWON CIKI: Yawan ciwon ciki alama ce da ke nuna mutun ya kamu da zazzabin typoid, zaka samu kanka da murdawar ciki, wani lokaci har da ciwon mara, zaka ji hanjin ka na kuka wani lokaci har sai mutun ya ziyarci bayi da sauran su.
RASHIN KUZARI: Mutun zai kasance akoyaushe ba shi da wani kuzari, aiki kadan zai yi sai gajiya.
Rashin jin dadin abinci yana daya daga alamomin kamuwar cutar typhoid
YANDA SANGA-SANGA KE MAGANCE ZAZZABIN TYPHOID
Masana maganin gargajiya sunyi gwaji akan yanda ganyen sanga sanga ke maganin zazzabin typooid.
Za asamu ganyen sanga sanga a wanke sa da ruwa masu tsabta, atafasa sa. Bayan an tafasa za a sauke a tace ganyen in ya huce a maida su ruwan sha.
Akan daka ganyen sa a tace ruwan ba tare da an tafasa ba.
Akan yi kunu da shi ana sha, ana kuma iya dafawa arika suraci da wanka da shi.
Bayan maganin ciwon typhoid da sanga sanga ke yi, bincike ya nuna cewa sanga sanga yana kashe kwayoyin plsmodium musamman falcifarum dake kawo zazzabin malaria na cizon sauro wato dai baya ga kasancewa sanga sanga na maganin typhoid to kuma yana maganin malaria.
RIKAKAFE
Mu kula da tsabtace muhallin mu, musanman ruwan shan mu, da kuma abincin mu. Mukan iya tafasa ruwan mu na sha kafin muyi amfani da su, wannan hanya ce sosai da za ta taimaka wurin rage yaduwar wannan ciwo. haka kuma rage cin abincin sayarwa Wanda ba a tabbatar da tsabtar sa ba.
Allah ya bamu lafiya yasa mu dace.
17 comments:
Allah ya saka da alheri. May Allah reward ur efford.
Ameen Abdul. Na gode!!
Thanks
Enter your comment...slm gaskiya naji dadin wannan bayani saboda na kashe kudi sosai akan typoid da malaria amma bayan yan kwanaki sai yadawo,insha ALLAH zan jarraba wannan Allah yasa muda ce
Allah Ya saka da alkhairi
Don Allah menene sanga sanga
Nagode daga mai bibiyarku da alheri
Don Allah menene sanga sanga?
Daga mai bibiyarku da alheri
Allah yaka
Don allah mene sanga
Dan Allah menene Sanga Sanga?
Don Allah ana iya amfani da yayan(seed) Rai dore don maganin thypoid da maleria
Thanks
Mashaa Allah
Salam naji dadin bayaninda kukayi sai naji wani yace za,a sharunda geak milk na tsawon kwana uku mene gaskiyen lamarin
Jazakallah
Masha Allah Allah yasaka
Allahu YA bada lada
Post a Comment